RFI Hausa
banner
ha.rfi.fr
RFI Hausa
@ha.rfi.fr
🌍 Sashen Hausa na RFI na maraba da ku a shafin Bluesky
💻 rfi.fr/ha/ 🎧 rfi.my/kai-tsaye
𝕏 rfi.my/Xha 📷 rfi.my/IGha 🗨️ rfi.my/WAha
Ɗumamar yanayi na ƙaruwa yayin da aka cika shekaru 10 da yarjejeniyar Paris
Ɗumamar yanayi na ƙaruwa yayin da aka cika shekaru 10 da yarjejeniyar Paris
Ƙwararrun kan ɗumamar yanayi sun yi gargaɗi dangane giɓin da ke ƙara girma na gaza cika alƙawuran ɗaukar matakai da kuma ta’azzarar matsalolin na Sauyin Yanayi, a daidai lokacin da Yanayin zafi ke ƙaruwa gami da yawaitar bala’o’in wutar daji da kuma ambaliya.
rfi.my
December 12, 2025 at 4:46 PM
An fitar da jerin ƴan wasa 28 da za su wakilci Najeriya a gasar cin kofin Afrika
An fitar da jerin ƴan wasa 28 da za su wakilci Najeriya a gasar cin kofin Afrika
Mai horas da tawagar Super Eagles ta Najeriya Eric Chelle, ya saki sunayen ƴan wasa 28 da zaije da su gasar lashe kofin Afrika AFCON da ƙasar Morocco za ta karɓi baƙunci.
rfi.my
December 12, 2025 at 4:19 PM
An fara shari’ar masu zanga-zanga 77 da aka kama a zaɓen Kamaru
An fara shari’ar masu zanga-zanga 77 da aka kama a zaɓen Kamaru
Kotu ta fara gudanar da shari’ar mutane 77 da aka kama, sakamakon zanga-zangar  da ta ɓarke bayan kammala zaɓen shugaban ƙasar Kamaru, wadda ta haifar da ruɗani da zulumi a faɗin ƙasar.
rfi.my
December 12, 2025 at 4:06 PM
Kotun ƙoli ta tabbatar da hukuncin kisa kan Maryam Sanda duk da afuwar Tinubu
Kotun ƙoli ta tabbatar da hukuncin kisa kan Maryam Sanda duk da afuwar Tinubu
Kotun ƙolin Najeriya ta tabbatar da hukuncin kisa kan Maryam Sanda da ta kashe mijinta, duk kuwa da afuwar da shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu ya yi mata. 
rfi.my
December 12, 2025 at 11:22 AM
Amurka ta sake aikewa da wakilai Rasha da Ukraine a ƙoƙarin sasanta ƙasashen
Amurka ta sake aikewa da wakilai Rasha da Ukraine a ƙoƙarin sasanta ƙasashen
Fadar gwamnatin Amurka ta ce a ƙarshen makon nan wani ƙarin wakilcin ƙasar na musamman zai sake tattaki zuwa gabashin Turai don ci gaba da tattaunawa a fatan da ake da shi na samar da yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Rasha da Ukraine.
rfi.my
December 12, 2025 at 9:48 AM
Majalisar ɗinkin duniya za ta yi zama da ɓangarorin da ke yaƙi a Sudan
Majalisar ɗinkin duniya za ta yi zama da ɓangarorin da ke yaƙi a Sudan
Sakatare Janar na majalisar ɗinkin duniya Antonio Guterres, ya ce za su gana da ɓangarorin da ke rikici da juna na Sudan a birnin Geneva, sai dai shugaban bai bayyana  ranar da za a yi wannan tattaunawa ba.
rfi.my
December 12, 2025 at 9:34 AM
Ghana ta haramta haƙar ma'adinai a gandun dajin ƙasar don kare muhalli
Ghana ta haramta haƙar ma'adinai a gandun dajin ƙasar don kare muhalli
Ma'aikatar muhalli, kimiyya da fasaha ta Ghana, ta sanar da haramta haƙar ma'adinai a cikin gandun dazukan ƙasar, a wani mataki da take ɗauka don kare sare itace da kuma rafuka daga bushewa.
rfi.my
December 12, 2025 at 9:20 AM
Ministan tsaron Najeriya ya yi umarni janye sojoji daga ilahirin titunan ƙasar
Ministan tsaron Najeriya ya yi umarni janye sojoji daga ilahirin titunan ƙasar
Ministan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa ya bada umarnin janye sojoji daga wuraren binciken ababan hawa da ke titunan sassan ƙasar, domin komawa yaƙi da ƴan ta'adda, inda ya ce ƴan sanda za su maye gurbin su wajen samar da tsaro a kan hanyoyin.
rfi.my
December 12, 2025 at 9:07 AM
Hukumar kula da wasannin Tennis ta Duniya ta dakatar da Quentin Folliot daga buga wasanni
Hukumar kula da wasannin Tennis ta Duniya ta dakatar da Quentin Folliot daga buga wasanni
Hukumar kula da wasannin Tennis ta Duniya (ITIA) ta dakatar da ɗan wasa Quentin Folliot daga buga wasanni har tsawon shekaru 20 bayan samun sa da laifin take dokokin wasa.
rfi.my
December 12, 2025 at 9:07 AM
Kotun Kenya ta dakatar da ƙasar daga ƙulla yarjejeniyar lafiya da Amurka
Kotun Kenya ta dakatar da ƙasar daga ƙulla yarjejeniyar lafiya da Amurka
Babbar kotun Kenya, ta baiwa gwamnatin ƙasar  umurnin dakatar da shiga yarjejeniyar kiwon lafiya da Amurka, shirin da zai laƙume sama da dala biliyan ɗaya da rabi har zuwa lakacin da za’a cika kaidojin doka.
rfi.my
December 12, 2025 at 7:59 AM
Dangote ya bada kashi 25 na dunkiyarsa domin bunƙasa ilimi a Najeriya
Dangote ya bada kashi 25 na dunkiyarsa domin bunƙasa ilimi a Najeriya
Shugaban kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya ƙaddamar da wani sabon shirin tallafawa ɗaliban Najeriya samun ilimi da zai ci naira triliyan guda da miliyan dubu 350 a cikin shekaru 10.
rfi.my
December 11, 2025 at 6:29 PM
Ƙasashen ECOWAS sun jaddada aniyar kare demokuraɗiyya da kare junansu
Ƙasashen ECOWAS sun jaddada aniyar kare demokuraɗiyya da kare junansu
Kasashen ECOWAS sun kara jaddada niyayyar su na zama tsintsiya madaurin ki daya wajen kare demokuradiyyar da kare mutuncin juna a duk sanda wata barazana ta kunno kai, musamman kamar yadda aka gani a yunƙurin juyin mulkin da aka yi a Jamhuriyar Benin.
rfi.my
December 11, 2025 at 4:42 PM
Manchester United ta sanar da ƙarin kudaden shigar da ta samu bayan sauye-sauye
Manchester United ta sanar da ƙarin kudaden shigar da ta samu bayan sauye-sauye
Babban jami'in gudanarwar Manchester United, Omar Berrada, ya yi ikirarin cewa kuɗin shigar da suka samu a baya-bayan nan ya nuna cewa suna samun ci gaba sosai, sakamakon sauye-sauyen da kulob ɗin ya yi.
rfi.my
December 11, 2025 at 4:42 PM
Wani Harin sojin Myammar a asibiti yayi sanadin mutuwar a ƙalla mutum 30
Wani Harin sojin Myammar a asibiti yayi sanadin mutuwar a ƙalla mutum 30
Aƙalla mutane 30 ne, suka rasa rayukansu sannan gommai suka jikkata, bayan wani hare haren  sojin Myammar da ya faɗa kan Asibitin garin Mrauk na jihar Rakhin, a yammacin ƙasar, ranar Laraba.
rfi.my
December 11, 2025 at 4:28 PM