RFI Hausa
banner
ha.rfi.fr
RFI Hausa
@ha.rfi.fr
🌍 Sashen Hausa na RFI na maraba da ku a shafin Bluesky
💻 rfi.fr/ha/ 🎧 rfi.my/kai-tsaye
𝕏 rfi.my/Xha 📷 rfi.my/IGha 🗨️ rfi.my/WAha
Benin: An kama tsohon ministan tsaro kuma ɗan tsohon shugaban kasa (Bony Yayi)
Benin: An kama tsohon ministan tsaro kuma ɗan tsohon shugaban kasa (Bony Yayi)
Jami’an tsaro sun kama ɗan tsohon shugaban Jamhuriyar Benin, kuma jagoran ƴan adawa,   Boni Yayi, da safiyar jiya Lahadi ba tare da bayyana wani dalili ba, mako guda bayan yunƙurin juyin mulkin da aka yi a ƙasar.
rfi.my
December 15, 2025 at 9:04 AM
Ƙawancen AES ya samar da bankin raya ƙasashen 3 da Sojoji ke mulka
Ƙawancen AES ya samar da bankin raya ƙasashen 3 da Sojoji ke mulka
Ƙawancen AES da ke ƙunshe da ƙasashen Nijar da Mali da Burkina Faso ya ƙaddamar da bankin raya ƙasashen 3 na BIDC ɗauke da jarin CFA biliyan 500 da nufin haɓɓaka tattalin arziƙi da ci gaban ƙasashen waɗanda dukkaninsu sojoji ke mulka.
rfi.my
December 15, 2025 at 8:23 AM
Kotun Kamaru ta aike mutane 30 gidan yari daga cikin 77 masu rikicin bayan zaɓe
Kotun Kamaru ta aike mutane 30 gidan yari daga cikin 77 masu rikicin bayan zaɓe
Bayan share tsawon makonni tsare a hannun ƴansanda, a ƙarshen makon jiya an gabatar da mutane aƙalla 77 da aka kama lokacin zanga-zangar da ta biyo bayan zaɓen shugabancin ƙasar Kamaru gaban kotu.
rfi.my
December 15, 2025 at 8:10 AM
Hari kan dandazon Yahudawa masu bikin Hanukka ya kashe mutane 16 a Australia
Hari kan dandazon Yahudawa masu bikin Hanukka ya kashe mutane 16 a Australia
Aƙalla mutane 16 ne suka mutu yayinda wasu 40 suka jikkata a wani harin ta’addanci da aka kai jiya Lahadi kan taron bikin masu ibada mabiya addininin Yahudanci a birnin Sydney na Australia, wanda mahukuntan ƙasar suka bayyana da harin ta’addanci.
rfi.my
December 15, 2025 at 7:56 AM
Ƴanbindiga sun kashe mutane 16 a wurin taron Yahudawa a Australia
Ƴanbindiga sun kashe mutane 16 a wurin taron Yahudawa a Australia
Adadin wadanda suka mutu a harin bindiga da aka kai wajen wani taron Yahudawa a gaɓar ruwan Bondi a Australia ya kai 16, a yayin da 40 da suka samu raunuka su na kwance a asibiti.
rfi.my
December 14, 2025 at 8:28 PM
An kama wani ɗan tsohon shugaban Jamhuriyar Benin bayan yunƙurin juyin mulki
An kama wani ɗan tsohon shugaban Jamhuriyar Benin bayan yunƙurin juyin mulki
Jami’an tsaro sun kama ɗan tsohon shugaban Jamhuriyar Benin, kuma jagoran ƴan adawa,   Boni Yayi, da safiyar jiya Lahadi ba tare da bayyana wani dalili ba, mako guda bayan yunƙurin juyin mulkin da aka yi a ƙasar.
rfi.my
December 14, 2025 at 5:59 PM
IGAD ta bayyana damuwa da matakin Eritrea na ficewa daga cikinta
IGAD ta bayyana damuwa da matakin Eritrea na ficewa daga cikinta
Ƙungiyar ci gaban ƙasashen gabashin Afrika ta IGAD ta bayyana damuwa da matakin Eritrea na ficewa daga cikinta ba tare da bin matakan da suka kamata ko kuma ƙorafi kan dalilin ficewar ba.
rfi.my
December 14, 2025 at 2:37 PM
WFP ta koka da ƙarancin tallafin abinci ga waɗanda yaƙi ya ɗaiɗaita a Sudan
WFP ta koka da ƙarancin tallafin abinci ga waɗanda yaƙi ya ɗaiɗaita a Sudan
Hukumar Abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya WFP ta yi hasashen fuskantar matsananciyar yunwa a sassan Sudan mai fama da yaƙi cikin wata mai kamawa sakamakon katsewar kuɗaɗen tallafin samar da abincin.
rfi.my
December 14, 2025 at 2:10 PM
Amurka ta zargi Rwanda da saɓa yarjejeniyar da ke tsakaninta da Rwanda
Amurka ta zargi Rwanda da saɓa yarjejeniyar da ke tsakaninta da Rwanda
Amurka ta zargi Rwanda da karya ƙa’idojin yarjejeniyar da aka ƙulla tsakaninta da maƙwabciyarta Jamhuriyyar Demokraɗiyyar Congo bayan hare-haren da mayaƙan M23 masu samun goyon bayanta suka ci gaba da kaiwa cikin Kigali.
rfi.my
December 14, 2025 at 1:43 PM
Dubban mutane na zanga-zangar neman firaministan Hungary ya sauka daga muƙaminsa
Dubban mutane na zanga-zangar neman firaministan Hungary ya sauka daga muƙaminsa
Dubban jama’a a ƙasar Hungary sun fito zanga-zanga a birnin Budapest, inda suke neman Firaminista Viktor Orban ya sauka daga muƙaminsa, bisa zargin gazawarsa wajen ɗaukar mataki kan yawaitar badaƙalar cin zarafin yara a ƙasar.
rfi.my
December 14, 2025 at 7:25 AM
Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi tir da harin da aka kaiwa jami'anta a Sudan
Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi tir da harin da aka kaiwa jami'anta a Sudan
Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi tir da harin wani jirgi mara matuƙi a Sudan da yayi sanadin mutuwar jami’anta na wanzar da zaman lafiya 6.
rfi.my
December 14, 2025 at 7:25 AM
Ana ci gaba da neman matashin da ya buɗewa ɗalibai wuta a Amurka
Ana ci gaba da neman matashin da ya buɗewa ɗalibai wuta a Amurka
Fiye da jami’an tsaro 400 aka jibge a yayin da ƴan sanda ke farautar wanda ake zargi da buɗe wuta kan ɗalibai a Jami’ar Brown da ke Rhode Island a Amurka, lamarin da ya yi sanadin mutuwar ɗalibai biyu tare da jikkata mutane tara.
rfi.my
December 14, 2025 at 6:58 AM
Eritrea ta sake sanar da ficewarta daga ƙungiyar IGAD ta ƙasashen gabashin Afrika
Eritrea ta sake sanar da ficewarta daga ƙungiyar IGAD ta ƙasashen gabashin Afrika
Ƙasar Eritrea ta sanar da ficewarta daga ƙungiyar ƙasashen Gabashin Afirka ta IGAD, tana mai zargin ƙungiyar da fatali da ƙa’idojin da aka kafa ta a kai da kuma gaza taka rawar gani wajen samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.
rfi.my
December 14, 2025 at 6:44 AM
Yau za'a buɗe taron ƙoli na ƙungiyar ECAWAS a Abuja
Yau za'a buɗe taron ƙoli na ƙungiyar ECAWAS a Abuja
Shugabannin ƙasashen Ƙungiyar Tattalin Arzikin Ƙasashen Yammacin Afirka ECOWAS sun hallara  a birnin Abuja na tarayyar Najeriya don buɗe babban taron ƙoli da za’a fara yau Lahadi.
rfi.my
December 14, 2025 at 6:31 AM
A karon farko an buɗe babban gidan tarin Libya da aka rufe bayan faɗuwar Gaddafi
A karon farko an buɗe babban gidan tarin Libya da aka rufe bayan faɗuwar Gaddafi
An sake buɗe gidan adana kayan tarihi na Libya, da ake kira As-Saraya Al-Hamra ko kuma Red Castle da ke birnin Tripoli, karon farko tun bayan boren da ya hambarar da gwamnatin Muammar Gaddafi, inda jama'a a yanzu za su samu damar shiga don ganin kayayyakin tarihin ƙasar.
rfi.my
December 13, 2025 at 7:57 PM
Mali ta kori sojan da ya wallafa littafin da ya fallasa cin zarafin da sojoji ke yi
Mali ta kori sojan da ya wallafa littafin da ya fallasa cin zarafin da sojoji ke yi
Rundunar sojojin Mali ta kori Kanal Alpha Yaya Sangare, wanda ya wallafa littafin da ya yi bayani dalla-dalla kan yadda sojoji ke cin zarafin jama'a.
rfi.my
December 13, 2025 at 5:55 PM
Majaliar ministocin ECOWAS sun nemi ƙungiyar ta samar da kuɗin bai daya
Majaliar ministocin ECOWAS sun nemi ƙungiyar ta samar da kuɗin bai daya
Majaliar ministocin ƙasashen yammacin Afrika da ke ƙarƙashin ECOWAS ta kammala tarota karo na 95, wanda ya tattaunawa kan harkokin tsaro da siyasa da kuma tattalin arzikin yankin.
rfi.my
December 13, 2025 at 5:28 PM
Sojin Najeriya sun kashe mayaƙan ISWAP da suka yi yunkurin kai hari a jihar Borno
Sojin Najeriya sun kashe mayaƙan ISWAP da suka yi yunkurin kai hari a jihar Borno
Dakarun Operation Hadin Kai da ke yaƙi da ta’addanci a shiyar Arewa maso Gabashin Najeriya, sun daƙile wani harin da mayaƙan ƙungiyar ISWAP suka kai a wani sansanin sojoji da ke garin Mairari a jihar Borno, inda suka kashe ƴan ta’adda da dama.
rfi.my
December 13, 2025 at 5:14 PM